Wata Baiwar Allah ta dabawa mijin ta wuka a kirji bayan sun samu sabani

Wata Baiwar Allah ta dabawa mijin ta wuka a kirji bayan sun samu sabani

Wata Mata mai shekaru 23 ta shiga hannun ‘Yan Sanda inda ake zargin ta da dabawa Mijin ta wuka. Sunan wannan Mata Damilola Ayeni kuma wannan abin takaici ya faru ne a cikin Garin Legas.

Wata Baiwar Allah ta dabawa mijin ta wuka a kirji bayan sun samu sabani

Wannan mata ta aika mijin ta lahira saboda kishi

Jaridar Punch ta rahoto cewa Damilola Ayeni ta hallaka mijin ta mai shekaru 36 a Duniya ne bayan rikici ya barke tsakanin su. Wannan Mata ta na zargin cewa mai gidan na ta yana cin amanar ta don haka rikici ya kaure har ta kai ga kisa.

Mahaifin Marigayin mai suna Sunday Ayeni ya bayyanawa ‘Yan Jarida cewa wannan mata tana zargin mijin na ta ne don haka fada ya kaure. Dama can ba a zaman lafiya a gidan auren na su kamar yadda surukin wannan mata ya bayyana.

KU KARANTA: Masu garkuwa sun saki Sheikh Al-Garkawy bayan karbar miliyoyin kudin fansa

Wata rana ne bayan Marigayin ya tashi aiki ya dawo gida sai Matar ta sa tace ta ji muryar mace tare da shi a lokacin da su kayi waya. Ana cikin haka ne ta daba masa wuka a kirji har ya mutu. Yanzu dai an karbe ‘Ya ‘yan su daga hannun ta.

Damilola Ayeni ta daba masa makami ne wanda ta sa aka sheka da shi asibiti domin a ceto ran sa, kafin a kai ko ina dai yace ga garin ku nan. Jama’a sun yi kokarin raba Ma’auratan a lokacin da su ke wannan rikici amma abin ya ci tura

Mahaifin mamacin wanda su ke aiki a wuri guda a wani asibiti a Legas yace shekaru 2 da su ka wuce aka daura masu aure kuma har sun samu ‘Ya ‘ya 2 amma kullum cikin rikici su ke. Ita dai matar tayi ikirarin cewa ta yi kokarin kare kan ta ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel