Akpabio: Harkar siyasa lissafi ce ba komai ba – Inji Minista Lai Mohammed

Akpabio: Harkar siyasa lissafi ce ba komai ba – Inji Minista Lai Mohammed

Mun samu labari cewa Gwamnatin Najeriya tayi magana game da batun sauya shekar da shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya watau Sanata Godswill Akpabio yayi zuwa APC.

Akpabio: Harkar siyasa lissafi ce ba komai ba – Inji Minista Lai Mohammed

Ministan labarai Lai Mohammed yace su na wa Akpabio lale

Tsohon Gwamnan na Akwa Ibom yana cikin manyan Majalisa kuma babba a Jam’iyyar PDP mai adawa ya tattara kayan sa ya fara shirin komawa Jam’iyyar APC. Ministan yada labaran kasar yace sun yi maraba da wannan.

Lai Mohammed yake cewa su na lale da baban Sanatan cikin tafiyar APC inda ya kara da cewa siyasa ‘yar cikin gida ce. Lai yace wadanda su ka fice daga APC sun yi haka ne don kashin kan su kuma sun yi banza inji Ministan.

KU KARANTA: An nemi Tambuwal ya sauka daga mukamin sa tun wuri

Ministan yada labarai da al’adu yace siyasa lissafi ce don haka duk da sun rasa wasu manyan Sanatoci a APC, yanzu sun karu bayan wasu ‘Yan Majalisa a Kudancin Kasar sun sauya-sheka sun dawo APC. Lai yace an yi canjaras.

Sai dai Ministan yace bai da masaniya ko za a nada Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawan kasar bayan ya dawo APC. Dama jiya kun ji cewa wani Babban Sanatan APC ya bayyana cewa za su tsige Bukola Saraki.

Jiya kun ji cewa an yi wata ganawa tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari daa shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattijawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom watau Godswill Akpabio a kasar Ingila inda Shugaban ke hutu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel