Mutane 5 da zasu iya maye gurbin kujerar mataimakin gwamnan Kano
- Sai ba wani sannan wani ke samu in ji masu iya magana
- Bayan ajiye aiki da tsohon mataimakin gwamna Farfesa Hafiz Abubakar yayi, rahotanni sun bayyana yadda wasu manyan 'yan siyasa ke zawarcin kujerar
Biyo bayan ajiye mukamin mataimakin gwamna da Farfesa Hafiz Abubakar yayi a Lahadin nan, wasu rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka mutane da yawa sun nuna bukatarsu akan samun wancan mukami na mataimakin gwamnan jihar Kano.
Wata Majiya ta bayyana cewa a kalla akwai mutane guda biyar da su ke harin wannan kujera ta mataimakin gwamna.
Cikin wadanda ake ganin zasu iya neman kujerar mataimakin gwamnan akwai kwamishinan yada labarai na jihar wato kwamared Muhammad Garba wanda tsohon shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa (NUJ), wanda kuma sun fito daga shiyya daya da tsohon mataimakin gwamna mai murabus.
KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan Kano ya fasa kwan dalilan da yasa yayi murabus
Sai kuma sabon kakakin majalisar dokokin jihar Kano wato Alhaji Kabiru Alhassan Rurum, wanda su ka fito shiyya daya da sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji.
Sai kuma tsohon shugaban majalisar dokokin jihar wato Yusuf Abdullahi Attah, a daya bangaren kuma akwai shugaban jamiyyar APC na jihar wato Abdullahi Abbas tare kuma da babban shehin Malamin nan Sheikh Ibrahim Khalil.
Akwai rahotanni masu karfi dake nuni da cewa kwamared Muhammadu Garba ka iya nasarar darewa kan kujerar mataimakin gwamnan jihar ta Kano, musamman idan aka yi la'akari da yadda ya ke caccakar manufofin tsohon gwamnan jihar Kano wato Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng