Kowa ya sai rariya: Sojoji sun damke wasu gayu 2 masu ci da guminsu

Kowa ya sai rariya: Sojoji sun damke wasu gayu 2 masu ci da guminsu

- Son gwaninta da kuma neman kudi ta hanyar damfara ya kai wasu matasa ya baro

- Bayan damfarar masu sha'awar shiga aikin Soja yanzu haka an cafke su

- Tuni idon Sojojin bogin ya raina fata

A yau Lahadi ne barikin Sojoji da ke Zaria ta yi holin wasu mutane 2 wadanda aka boye sunayensu ga manema labarai a matsayin masu yin sojan gona da kuma damfarar mutane ta hanyar karbe musu kudi da nufin za su samar musu da aikin soja.

Kowa ya sai rariya: Sojoji sun damke wasu gayu 2 masu ci da guminsu
Kowa ya sai rariya: Sojoji sun damke wasu gayu 2 masu ci da guminsu

Da ya ke holar ta su, jami'an hulda da yan jama'a na barikin Sojin laftanar Adekunle Adeyemi ya bayyana cewa mutanen suna Sojan gona ne a matsayin jami'an Sojoji.

Ya kara da cewa suna samu rahotanni akan faruwar irin wannan al'amarin a duk lokacin da za'a dauki sababbin Sojoji, akan samu masu yin Sojan gona tare da karbar makudan kudade daga hannun wasu da nufin samar musu da aikin na Soja.

KU KARANTA: Kaki ba leda ba: Wani saurayi zai shafe wata 10 a garkame saboda yin Sojan gona

“An Jawo hankalinmu akan abin da yake faruwa dangane da irin wannan al'amarin a cikin birnin Zaria, inda aka samu wasu bata garin da suke Sojan gona, inda hakan zai kawo bacin suna da zubewar mutunci da kuma kimar makarantar horon Sojojin".

“Su kanyi amfani da shafukan sada zumunta wajen yaudarar mutane masu sha'awar aikin soja tare da kwadaita musu cewa za su taimakesu su samu aikin, amma sai sun bayar da kudade".

Adeyemi ya kara da cewa jami'an ‘yan sandan Sojoji ne su kayi nasarar cafke mutanen da ake zargin.

Kowa ya sai rariya: Sojoji sun damke wasu gayu 2 masu ci da guminsu
Kowa ya sai rariya: Sojoji sun damke wasu gayu 2 masu ci da guminsu

Ya kuma tabbatar da cewa a lokacin da suka samu nasarar damke su, abin da suka samu a hannunsu ya kai Naira 163,000.

“Amma sun tattara kudi sama da Naira miliyan daya a hannun mutane 8 da suke son shiga aikin soji"

A bangaren wadansu da aka damfara mazauna unguwar Rigasa sun bayyana cewa mutanen sun karbi kimanin Naira 250,000 da nufin sama masU aikin Soja.

A karshe jami'an na hulda da jama'a na makarantar horon Sojin ya bayyanawa al'umma cewa tsarin daukar aikin Sojan kyauta ne, domin ba sa karbar sisin kowa kafin daukarsa aikin. Sannan yayi kira ga al'umma su mayar da hankali tare da yin taka tsan-tsan akan aikin masu zamba cikin aminci don gujewa fadawa hannun ‘yan damfara.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel