Rikicin Kaduna: APC ta soke dakatar da Sanata Shehu Sani daga Jam’iyya

Rikicin Kaduna: APC ta soke dakatar da Sanata Shehu Sani daga Jam’iyya

- Jam’iyyar APC ta cire dakatarwar da aka yi wa Sanatan Tsakiyar Kaduna

- Uwar Jam’iyyar APC tace a dawo da Sanata Shehu Sani cikin Jam’iyyar

- Shugaban Jam’iyyar yayi haka ne domin a zauna lafiya a Jihar Kaduna

Kwanaki kun ji labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki da ke karamar Hukumar Kaduna ta Kudu ta dakatar da Sanatan Yankin. Yanzu dai uwar Jam’iyya tayi watsi da wannan mataki da aka dauka.

Rikicin Kaduna: APC ta soke dakatar da Sanata Shehu Sani daga Jam’iyya
An dawo da Sanata Shehu Sani cikin Jam'iyyar APC

Sakataren yada labaran Jam’iyyar APC na rikon kwarya Yekini Nabena ya bayyana cewa Shugabannin Jam’iyyar APC ta janye dakatarwar da aka yi ‘Dan Majalisar Dattawan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya watau Sanata Shehu Sani.

KU KARANTA: Hatsarin mota ta ritsa da wani 'Dan Majalisa a Kano

Yekini Nabena ya bayyana wannan ne yau dinnan inda Uwar Jam’iyyar ta nemi Shugaban APC na Mazabar Sanata Shehu Sani watau Alhaji Ibrahim Salisu Togo yayi biyayya ga matakin da Jam’iyyar ta dauka domin dinke baraka a Kaduna.

Uwar Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne domin ganin an shawo kan rikicin da ake yi tsakanin Sanatan na Kaduna ta tsakiya da kuma Gwamnan Jihar sa watau Nasir El-Rufai. Dama ba a ga maciji tsakanin manyan ‘Yan siyasar Jihar.

Yanzu dai Majalisar NWC na Jam’iyyar APC karkashin Adams Oshiomhole ta dawo da Shehu Sani cikin Jam’iyyar bayan an horar da shi a baya saboda sukar Gwamnatin Nasir El-Rufai da kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yake yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng