Dalilan da yasa dole matasan mu su shiga harkar siyasa - Fadar Shugaban Kasa

Dalilan da yasa dole matasan mu su shiga harkar siyasa - Fadar Shugaban Kasa

An bukaci matasa da su dage zange wurin shiga harkar siyasa a kasar nan, domin kuwa daga nan ne kawai zasu iya kawo wa kasar nan cigaban da ake bukata

Dalilan da yasa dole matasan mu su shiga harkar siyasa - Fadar Shugaban Kasa

Dalilan da yasa dole matasan mu su shiga harkar siyasa - Fadar Shugaban Kasa

Mr Tolu Ogunlesi, mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa akan kafafen watsa labarai, ya bukaci matasan Najeriya dasu shiga cikin harkar siyasa in har suna son bawa kasar nan gudummawa.

Ogunlesi yayi maganar ne a kashi hudu na taron karawa juna sani a wata makaranta dake Ibadan.

DUBA WANNAN: Labarin wata DPO, da yanda barayi suka yi mata tsirara a kasuwa

Ogunlesi yace dole ne matasan Najeriya su yi amfani da damar da suka samu don cimma manufofin su.

"Dukkanin mu alhakin tabbatar da wannan kudurin ya rataya a wuyan mu. Duk abinda muka samu a matsayin cigaba, dole ne mu rungume shi," inji shi.

Wadanda suka yi bayani a taron sun hada da Mista Eze Onyekpere, Daraktan Centre for social justice a Najeriya da Mrs Edem Ossai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel