Sheikh Pantami yayi magana game da sace aminin sa da 'yan bindiga sukayi a Kaduna

Sheikh Pantami yayi magana game da sace aminin sa da 'yan bindiga sukayi a Kaduna

Biyo bayan labarin satar fitaccen malamin nan na jihar Kaduna tare da daliban sa, Sheikh Ahmad Adam Algarkawiy da ya bazu a gari da kafafen yada labarai, aminin sa Sheikh Pantami yayi magana.

Sheikh Pantami dake zaman shugaban hukumar nan ta fasahar zamani ta gwamnatin tarayya ya yi roko ga Allah Subhanahu Wata'ala da ya kubutar da malamin daga dukkan sharrin na masu garkuwa da mutane.

Sheikh Pantami yayi magana game da sace aminin sa da 'yan bindiga sukayi a Kaduna
Sheikh Pantami yayi magana game da sace aminin sa da 'yan bindiga sukayi a Kaduna

KU KARANTA: Wani na hannun damar Buhari ya shirya ficewa APC a Ondo

Legit.ng ta samu cewa a jiya ne dai 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba suka dira a makarantar da Sheikh Ahmad Adam din ke koyarwa suka kuma yi awon gaba da shi tare da daliban sa.

Shehin malamin ya kuma yi addu'ar samun dauki daga Allah dangane da matsalar tabarbarewar tsaro a kasar baki daya.

Mun samu tsokacin nasa ne dai daga wani runutu da ya wallafa a shafin sa na dandalin zumunta na Facebook.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng