Sauya Sheka: Saraki zai san makomarsa da taimakon sanatoci - APC
Jam’iyyar All Progressives Congress ta bayyana cewa sanatoci za su sanar da makomar Saraki imma zai ci gaba da rike matsayinsa a matsayin shugaban majalisar dattawa ko akasain haka.
Jam’iyyar tace har gobe ita ce zabin dukkanin masu siyasar gaskiya kamar yadda bazata yadda a lalata shirin da mambobinta suka dade sunayi har ta kai wannan matsayi.
Mataimakin Shugaban shuganan APC na kasa (Kudu maso kudu), Hilliard Eta, ya bayyana hakan yayinda yake maida martani ga zargin da ake yin a cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party na shirin tursasa haifar da chanji a shugabancin majalisar dattawa.
KU KARANTA KUMA: Sauya shekar Saraki, Tambuwal da sauransu ya sabama kundin tsarin mulki - Falana
Ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, ga watan Agusta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng