Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta halarci gagarumin taro a kasar Burkina Faso (hotuna)
Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ta halarci wani babban taro kan cutar daji a Ouagadougou, Burkina Faso.
An gudanar da taron ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta, sannan an shirya taro ne ga mambobin kungiyar Musulmai na Afrika wato Africa Group of the Organisation of Islamic Cooperation.
A cewar uwargidan shugaban kasar, ita da sauran matan shugabannin kasashen Afrika sun shirya wayar da kan mutane kan hanyoyin hana cutar kansa a kasashe daban-daban.
Ta kuma yi godiya ga uwargidaan shugaban kasar Burkina Faso, Misis Sika Kabore kan kyakyawar tarba da ta shirya masu.
Ga hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Karin matsayi: An nada Saraki a matsayin uban jam’iyyar PDP na kasa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng