Masifa ba’a sa miki rana: Yadda wani Tankin ruwa ya diro akan Motoci

Masifa ba’a sa miki rana: Yadda wani Tankin ruwa ya diro akan Motoci

Hatsari aka ce ba sai a Mota ba, kuma dama ai tsautsayi ba’a sa masa rana, wannan shine kwatankwacin lamarin da ya faru a garin Asaba na jihar Delta, inda wani tankin ruwa ya fado akan wasu Motoci dake ajiye, kamar yadda gidan talabijin an Channels ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, a dandan wasanni na garin Asaba, inda Tankin dake baiwa kwamin gasar wanka ruwa ya fado, sakamakon gazawa da karafan dake rike shi suka yi.

Masifa ba’a sa maki rana: Yadda wani Tankin ruwa ya diro akan Motoci
Tanki

KU KARANTA: Ba zan cuceku ba, ba kuma zan yarda wani ya cuceku ba – Buhari

Wannan lamari ya faru ne kwana daya da kammal gyaran wannan dandalin wasa na Stepehen Keshi don ya karbi baki da zasu fafata a gasar wasannin zakarun Afrika karo na 21.

Sai dai rahotanni basu ruwaito asarar rai ko jin rauni ba, ga dai hotunan hadarin nan.

Masifa ba’a sa maki rana: Yadda wani Tankin ruwa ya diro akan Motoci
Hadari

Masifa ba’a sa maki rana: Yadda wani Tankin ruwa ya diro akan Motoci
hadari

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: