Yanzu Yanzu: Tambuwal ya halarci taron masu ruwa da tsaki na PDP
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, Samuel Ortom na jihar Sokoto, da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun halarci taron kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Peoples Democratic Party a Abuja.
Tsohon shugaban jam’iyyar, Cif Barnabas Gemade da kuma jakadan Najeriya a kasar Afrika ta kudu, Alhaji Ahmed Ibeto suma sun hallara a wajen taron.
Ana gudanar da taron ne a sakatariyar PDP na kasa dake Abuja.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugabannin kananan hukumomi, kansiloli sun sauya sheka daga APC zuwa PDP
Dukkaninsu sun sauya sheka ne daga APC zuwa PDP a yan kwanakin nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng