Kashe-kashe: Ni kwararren Mafarauci ne kuma ko yau ta kama sai in shiga Daji – Kazaure

Kashe-kashe: Ni kwararren Mafarauci ne kuma ko yau ta kama sai in shiga Daji – Kazaure

‘Dan Majalisar da ke wakiltar Yankin Kazaure da Roni da Gwiwa da kewaye a Jigawa Muhammad Gudaji Kazaure ya nemi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi masa izini yayi maganin wadanda ke kashe mutane a irin su Zamfara.

Kashe-kashe: Ni kwararren Mafarauci ne kuma ko yau ta kama sai in shiga Daji – Kazaure

Honarabul Gudaji Kazaure yace akwai hannun ‘yan siyasa a kashe-kashe

Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana cewa duk da yana Majalisa amma a shirya yake da ya shiga inda ake kashe-kashe a Najeriya domin maganin masu wannan danyen aiki da ke batawa Gwamnatin nan suna.

KU KARANTA: Honarabul Gudaji Kazaure ya caccaki wadanda su ka bar APC

Kazaure ya nemi Shugaba Buhari ya hada shi da Jami’an tsaro domin ya shiga sako-sako na inda ake tada rikici a kasar nan domin zakulo wadanda ke wannan barna. ‘Dan Majalisar yace akwai sa hannun ‘yan siyasa a lamarin.

Hon. Gudaji Kazaure ya bayyana cewa akwai wasu ‘Yan siyasa da ke hura wutan rikicin da ke aukuwa a Najeriya. Wani ‘Dan Majalisa daga Yankin Jihar Filato dai ya fasa kwai inda yace wasu manya na da hannu a rikicin da ake yi.

Jiya kun ji cewa ‘Dan Majalisar yayi Allah-wadaran ‘Yan siyasan da su ka fice daga APC. Kazaure yace sun cuci Talakawan da su ka zabe su kuma sai sun ciza yatsa a zabe mai zuwa na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel