Wani babban na-kusa da Kwankwaso ya bayyana abin da ya sa su ka koma PDP

Wani babban na-kusa da Kwankwaso ya bayyana abin da ya sa su ka koma PDP

Labari ya bayyana mana game da abin da ya sa tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya-sheka daga Jam’iyyar APC ya koma PDP daga bakin wani babban Hadimin sa Kwamared Aminu Abdussalam.

Aminu Abdussalam yayi hira da gidan rediyon Xpress ta Kano a wani shirin siyasa da Salamatu Sabo Bakin-Zuwo ta shirya kwanaki. Tsohon Kwamishinan na Kwankwaso yace ba yau Sanatan ya fara yaki domin Talakawan kasar nan ba.

Wani babban na-kusa da Kwankwaso ya bayyana abin da ya sa su ka koma PDP
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Aminu Abdussalam ya kawo lokuta da dama da Kwankwaso ya tashi zuwa Kudancin Najeriya domin kare martabar ‘Yan Arewa da ake ci wa mutunci. Abdussalam yace Kwankwaso ne babban da ya fi kare hakkin Arewa a lokacin Jonathan.

Tsohon Kwamishinan harkokin gidan Gwamnati Aminu Abdussalam ya bayyana cewa irin saba alkawarin da APC tayi da yunwa da tsadar rayuwa da kashe-kashen rayuka da ke faruwa a Gwamnatin nan ta sa su ka bar Jam’iyyar APC.

Babban Hadimin ‘Dan Majalisar ya bayyana cewa wannan Gwamnati ba ta jin shawarar su sannan kuma sam Shugaban Kasa Buhari ba ya sauraron su ko a zauna don haka babu dalilin cigaba da zama a tafiyar da ba ta da wani alamun bullewa.

KU KARANTA: Fitaccen Sanatan Arewa da ke shirin takarar shugaban kasa ya tara Jama’a a Katsina

Kwamared Abdussalam yace Shugaba Buhari ne yace Kwankwaso yayi takarar Shugaban kasa a karkashin APC a 2014. ‘Dan Kwankwasiyyar ya kuma nuna cewa Kwankwaso bai da niyyar sake neman takarar Sanata a zabe mai zuwa.

Abdussalam ya bayyana cewa Kwankwaso yayi kokarin nunawa Buhari matsalar da siyasar Kano ta shiga cikin tun a tuni amma yayi murus bai yi wani abu ba. Wannan dai ya sa Kwankwaso da sauran Mabiyan sa su ka sauya sheka.

Kwanakin baya ne Shugaba Buhari ya zauna da Kwankwaso ana daf da zai bar Jam’iyyar bayan sun yi bakin kokarin su a baya na ganawa da shi amma bai yiwu ba. Aminu Abdussalam yace ba manufar kan sa ce ta sa su ka bar APC ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel