Wani ‘Dan Majalisa yayi taurin-kai ya ki bin Gwamnan Jihar Kwara zuwa PDP

Wani ‘Dan Majalisa yayi taurin-kai ya ki bin Gwamnan Jihar Kwara zuwa PDP

Idan ku na biye da siyasar Najeriya kun san cewa ‘Yan Majalisar dokokin Jihar Kwara sun bi sauran shugabannin Jihar zuwa Jam’iyyar PDP mai adawa bayan sun fice daga APC a makon nan.

Wani ‘Dan Majalisa yayi taurin-kai ya ki bin Gwamnan Jihar Kwara zuwa PDP
Gwamnan Jihar Kwara da manyan 'Yan APC sun koma PDP

‘Yan Majalisu 23 cikin Majalisar mutum 24 da ke wakiltar Mazabun Jihar Kwara sun sauya-sheka zuwa Jam’iyyar adawa bayan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamnan Jihar Abdulfatahi Ahmad sun bar APC.

Kakakin Majalisa Dr. Ali Ahmad ya bayyana cewa ‘Yan Majalisa har 23 sun sauya sheka bayan ganin Jam’iyyar APC ta gaza taka wani rawar gani. Sai dai akwai Saheed Popoola wanda shi kadai ne ya rage bai koma PDP ba.

KU KARANTA: APC ta sanar da nadin sabon Sakataren yada labarai na Jam’iyya

Honarabul Saheed Popoola wanda ke wakiltar Mazabar Ojomu-Balogun a Yankin Offa yayi zaman sa da-ram-dam-dam a Jam’iyyar APC. ‘Dan Majalisar yayi mursisi yace shi ba zai bar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.

Duk da karfin tsohon Gwamnan Jihar kuma Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki a siyasar Kwara, ana tunanin bai da karfi sosai a Yankin Offa. Tun tale-tale dai Bukola Saraki ba ya samun nasara yadda ya saba a Garin na Offa.

A dalilin haka ne ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Yankin ya ki bin Gwamnan Jihar Kwara da Shugaban Majalisar Dattawa zuwa PDP. Yanzu dai tuni har an tsige Saheed Papoola a matsayin shugaban kwamitin wasanni a Majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng