Wannan rayuwa: Tsananin talauci ya sanya wata kaka ta siyar da jikarta
- An yi cinikin wata jaririya tu tana cikin uwarta a jihar Akwa Ibom
- Kakar mai cikin ce tayi wannan danyan aikin da sunan ragewa 'yarta ta wahalar kuncin rayuwar da suke ciki
- Amma sai dai kashe kafin fadawar ciki 'yan sanda suka cafke su
Jami'an hukumar ‘yan sanda na kasa reshen jihar Akwa Ibom sun cafke wata mata bisa laifin sacewa tare da sayar da jikarta akan kudi Naira 200,000.
Matar mai suna Ekaette Obot, an zarge ta ne da sace jikarta tare kuma da sayar da ita akan zunzurutun kudi kimanin naira 200,000.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa Matsin rayuwa gami da talauchi ne ya sanya Ekaette Obot daukar wannan danyen hukuncin.
KU KARANTA: Wani hatsabibin dan kungiyar asiri ya fada komar 'yan sanda
"Na yanke hukuncin sayar da jikar tawa ne, saboda raba ya ta mai suna Blessing Okon mai kimanin shekaru 18 a duniya daga kangin talaucin da ta ke ciki" In Ji Ekaate Obot
A nasa bangaren kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Akwa Ibom Adeyemi Ogunjemilusi ya bayyana cewa sun garkame matar ne bisa laifin sayar da jaririyar da ba'a haifa ba tun tana ciki.
"Wannan Matar wacce ta kasance mahaifiya ce ga Blessing tana da niyyar sayar da jikarta da zarar an haifeta akan kudi kimanin Naira 200,000, domin ta bayyana hakan ne da bakinta" In ji kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Akwa Ibom.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng