Jam’iyyar APC ta dauki matakan ladabtar da shugaban majalisar dattawa

Jam’iyyar APC ta dauki matakan ladabtar da shugaban majalisar dattawa

Awanni kadan bayan ficewar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki daga Jam’iyyar APC, uwar jam’iyar APC ta bayyana cewar ta aika masa da wasikar gargadi, tare da shaida masa za taladabtar da shi matukar bai kare kansa a gabanta ba.

Legit.ng ta ruwaito APC ta sanar da haka ne cikin wata sanarwar data fitar a ranar Talata, 31 ga watan Yuli, wanda ta samu sa hannun sakataren jam’iyyar, Mai Mala Buni, insu suka zargi Saraki da yi ma sashi na 21 na kundin dokokin jam’iyyar tare da yi ma Jam’iyya zagon kasa.

KU KARANTA: Likafa ta cigaba: Shugaba Buhari ya zama shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka

APC tace Saraki ya ne yayi kutun kutun da ya yi sanadiyyar ficewar wasu Sanatocin jam’iyyar zuwa jam’iyyun adawa, haka zalika a matsayinsa na shugaban jam’iyya, Saraki ya ki ya tantance mutanen da shugaba Buhari ya aika masa don nada su mukamai, kuma yayan jam’iyyar APC ne.

“Wannan lamari ya kunyata jam’iyyar APC, tare da cin mutuncin jam’iyyar” Inji APC. Bugu da kari, Jam’iyyar ta zargi Saraki da jan kafa akan duk kasafin kudin da shugaba Buhari ya kai musu don tantancewa, wanda hakan ya kawo tsaiko ga ayyukan gwamnati.

Daga karshe APC tace duk kokarinda ta yin a ganin ta sulhunta tsakaninta da wasu Sanatoci da suke ganin an saba musu, amma Saraki ya dakile wannan shiri, sa’annan tace ya shirya gangamin nuna adawa da jam’iyyar a jihar Kwara.

Daga karshe APC ta bukaci Saraki ya amsa wadannan zarge zarge cikin awanni 48, idan kuma ba haka ba, zai fuskancin matakan ladabtarwa akansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
APC