‘Yar biloniya Mairama Indimi ta auri mai gidanta a kasar Faransa

‘Yar biloniya Mairama Indimi ta auri mai gidanta a kasar Faransa

Mairama, ýa ga shahararren dan kasuwar man fetur Mohammed Indimi da mijinta, Mustafa Marcus Masango sun yi tsadadden bikin aurensu a ranar Asabar, 28 ga watan Yuli a kasar Faransa.

Mairama da angon nata, Marcus sun ci gaba da bikin aurensu ta hanyar shirya hadadden liyafar aure.

Tuni dai dama ma’auratan sunyi bikin al’ada da daurin aure a watan Disamban 2017 a katafaren gidan mahaifinta dake Maiduguri.

Hotunan wannan aure na turawa da suka yi a bayan nan ya yi fice a yanar gizo inda Mairama ta sanya kayan auren turawa wadda yayi matukar amsarta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta wanke Bafarawa daga tuhumar da ake masa na rashawar N15b

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng