Saudiyya ta baiwa wani kamfani damar gina gidajen Sinima guda 30 a fadin kasar

Saudiyya ta baiwa wani kamfani damar gina gidajen Sinima guda 30 a fadin kasar

Hukumar raya al'adu da sadarwa ta kasar Saudiyya ta bayyana cewar ta baiwa kamfanin Al-Rashid Empire Cinema damar gina gidajen Sinima guda 30 a kasar, wanda ake saka ran za a kamalla a cikin shekaru 3

Saudiyya ta baiwa wani kamfani damar gina gidajen Sinima guda 30 a fadin kasar

Saudiyya ta baiwa wani kamfani damar gina gidajen Sinima guda 30 a fadin kasar

Hukumar raya al'adu da sadarwa ta kasar Saudiyya ta bayyana cewar ta baiwa kamfanin Al-Rashid Empire Cinema damar gina gidajen Sinima guda 30 a kasar, wanda ake saka ran za a kamalla a cikin shekaru 3.

DUBA WANNAN: Wani mummunan hadari yayi sanadiyyar mutuwar mutum 6, yayinda 69 suka ji munanan raunuka

Ministan al'adu da sadarwa na kasar Awwad bin Salih Al-Awwad ya bayyana cewar, kamfanin Al-Rashid shine kamfani na uku da aka baiwa damar ginin Sinimar, bayan kamfanunnukan "American Multi-Cinema" (AMC) wanda ke kasar Amurka da kuma kamfanin VOX Cinema wanda ke hadaddiyar daular Larabawa.

A watan Disambar shekarar data gabata ne ma'aikatar ta bayyana cewar kasar ta bata lasisin gina gidajen Sinima a fadin kasar, kuma a ranar 18 ga watan Afrilun wannan shekarar ne aka bude gidan Sinima na farko a kasar ta Saudiyya, inda a yanzu haka an fara kallon fina - finai a cikinsa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel