Yan sanda sun kama mutane 43 dake garkuwa da mutane, fashi da makami da sauransu a Abia
Rundunar yan sandan Abia sun kama mutane 43 dake aikata laifuka daban-daban ciki harda garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, da fyade cikin kwanaki 40.
Kwamishinan yan sandan jihar, Mista Anthony Ogbizi ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake ganawa da manema labarai a Umuahia a kokarin rundunar na magance laifuka a jihar.
Ogbizi ya bayyana cewa kamun ya kasance ne sakamakon kokarin da rundunar ke yin a tabbatar da zaman lafiya da rage laifuka a tsakanin jama’a.
Ya kuma alakanta kamun da ingancin dangantaka tsakanin yan sanda da kungiyar yan banga na jihar.
KU KARANTA KUMA: Adamu na hari na ne don ya kare kansa daga EFCC – Saraki
Kwamishinan ya bukaci jama’a musamman masu mota da su dunga kula cewa masu laifi sun samo sabbin hanyoyin satar motoci.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng