Shugaban Facebook Mark Zuckerberg ya rasa Dala Biliyan 17 daga cikin kudin sa

Shugaban Facebook Mark Zuckerberg ya rasa Dala Biliyan 17 daga cikin kudin sa

A makon jiya ne Mark Zuckerberg wanda yana cikin manyan Attajirin Duniya ya rasa abin da ya haura Dala Biliyan 16 a cikin kankanin lokaci. Wannan kudi dai sun fi karfin Naira Tiriliyan 5.

A Ranar Laraba da ta wuce ne mu ka samu labari cewa Mark Zuckeberg ya rasa Dala Biliyan 17 a cikin kudin da ya mallaka a Duniya. Duk da yawan wannan kudin dai ba su kai kashi 1 na 5 din abin da Matashin ya ke da su ba.

Shugaban Facebook Mark Zuckerberg ya rasa Dala Biliyan 17 daga cikin kudin sa
Mark Zuckerberg yayi asarar Tiriliyan 5 a cikin kwanaki biyu

Hannun jarin kamfanin nan sada zumunta na Facebook ne ya fadi kasa wanda ya sa ribar Kamfanin na bana ya ragu ainun. Abin da Zuckerberg ya rasa sun haura gaba daya dukiyar Aliko Dangote wanda ya fi kowa kudi a Afrika.

KU KARANTA: Manyan Attajiran mata 3 da su ka zarce kowa dukiya a 2018

Kwanakin baya da kasuwa tayi kyau Mark Zuckerberg ya samu Dala Biliyan 3 wanda idan aka yi lissafi zai haura sama da Naira Tiriliyan guda. A lokacin nan sai da arzikin Mark Zuckerberg ya doshi sama da Dala Biliyan 66.

Abin da Dangote ya mallaka dai bai wuce Dala Biliyan 12. Yanzu ‘Dan Matashin watau Mark Zuckerberg ne mutum na 3 a jerin kudi a Duniya. Jeff Bezos wanda ya ba Dala Biliyan 150 baya da Bill Gates duk sun sha gaban sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng