Na fadama Shehu Sani kada ya sauya sheka zuwa PDP – Balarabe Musa
Tsohon gwamnan jihar Kadiuna, Balarabe Musa, yace shi bai ce kada Shehu Sani ya bar APC amma kada ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party.
Shehu Sani ya bayyana cewa Musa, shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole da Bola Tinubu na daga cikin wadanda suka rarrashe sshi da kada ya bar APC zuwa jam’iyyar adawa, PDP.
Tsohon gwamnan ya fadama majiyarmu ta Premium Times wayar tarho a safiyar ranar Lahadi cewa “Na fada masa cewa kada ya sauya sheka daga jam’iyyar inda PDP zai koma.
"Ban ce kada ya bar APC ba. Kawai na dai ce masa kada ya sauya sheka zuwa PDP.”
KU KARANTA KUMA: Sanatocin da suka sauya sheka masu aikata rashawa ne, kuma suna tsoron a kama su idan Buhari ya sake cin zabe – El-Rufai
Shehu Sani na daga cikin wadanda aka zata za su sauya sheka daga APC sai dai sanatan ya ba da mamaki bayan yace ya canza shawara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng