Hukumar NAFDAC ta dakile wata babbar annoba da aka so shigowa da ita kasar nan
- Sauran kiris a shigo da wasu gurbatattun kaya Najeriya
- Sai dai hukumar NAFDAC tayi nasarar cafke su kafin hakan ta afku
- Amfani da kayan da wa'adin ingancinsu ya kare na iya nakasa ko kashe wanda yayi ta'ammali da su
Hukumar Lura da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDC) ta kama rubabbun kayan ganyayyaki da dangoginsu da nauyinsu ya kai kilogiram 3,300 na kamfanin PINGIUN.
Babbar Daraktan hukumar Farfesa Mojisola Uku ce ta bayyana hakan ga manema labarai cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin a birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Aikin Hajji: Saudiyya zata rage gurbin mahajjatan Najeriya a shekara mai zuwa saboda dalili 1 tak
Daraktan ta kara da cewa ta samu bayanin sirri ne kan shigowa rubabben kayan lambun ne tun a watan Yuli daga hukumar kula da tsaftar abinci ta kasa wato FSAN, inda jami'an hukumarta da ke fadin kasar nan suka himmatu wajen ganin sun dakile tare da kame wadannan gurbatattun kayan lambun da zarar an shigo da su kasar nan.
“Amfani da gurbatattun kayan abinci ko na sha ga al'umma kan haifar da mummunar illah ga jikin bil-Adama ko dabbobi, wanda hakan kan kai ga asarar rayuka" in ji Adeyeye.
Ta kuma kara da cewa wadannan kayan lambun da hukumarta ta kama za'a lalata su ne domin haka ne kadai zai kara bayar da kariya ga yan kasar nan.
A karshe kuma ta shawarci al'umma a duk inda su ke a fadin kasar nan da su yi kokarin mika dukkanin wani kayan lambu na kamfanin PINGUIN, nusamman wanda aka yi su a ranar 13 ga watan Agusta na Shekarar 2016 zuwa ranar 20 ga watan Yunin Shekarar 2018 zuwa ga ofishin hukumar NAFDAC mafi kusa da su
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng