Karen hauka ya ciji wani matashi, ya kashe Ubansa da kaninsa
- Wani matashi ya aikata aika-aika a wani kauye dake jihar Ebonyi
- Saurayin ya kashe mahaifinsa da kanwarsa sanna ya sassari wasu makwabtansu don sun zo hana shi aikata mugun aikin da yayi niyya
A ranar Lahadi ne wani kauye dake jihar Ebonyi suka waye gari cikin tashin hankali da rudani na kisan kai da Julius Nwode dan shekaru 25 ya yiwa mahaifinsa da kanwarsa.
Al'amarin ya faru ne a kauyen Ifelemu dake karamar hukumar Ikwo na jihar ta Ebonyi.
Wani wanda ya bayar da shaidar yadda lamarin ya faru ya shaidawa manema labarai cewa matashin ya shigo cikin fushi ne inda ya farwa mahaifinsa da kanwarsa sannan ya dawo kan wasu makota da suka yi yunkurin shawo kansa.
"A lokacin da yake saran mahaifin nasa da adda sai ‘yar uwarsa ta shigo tana mai kokarin ganin ta hana shi, nan take ita ma ya sassarata ta fadi mataciyya".
"wasu makota da suka ga abinda ya faru sun yi kokarin ganin sun hana shi aikata wannan aika-aika nan take su ma ya far musu da sara.
A lokacin da Julius yake kokarin barin kauyen, sai wani mutum mai suna Peter wanda matarsa na daya daga cikin wadanda Julius ya sara yayinda suke kokari ganin sun hana shi cimma burinsa. Nan take Peter ya shiga cikin gida ya dauko bidiga ya harbe shi har lahira".
KU KARANTA: Abin Al-ajabi: Wata mata ta haifi 'yan biyar rigis cikin damuna
An mika gawawwakin wanda suka rasu zuwa asibitin koyarwa na Abakaliki, wanda suka samu rauni kuwa ana cigaba da basu kulawa a wani asibiti wanda ba a bayyana sunansa ba.
Mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar Loveth Odah ta tabbatar da faruwar lamarin.
"Yaron mai shekaru 25 ya shigo da gatari da adda a hannunsa ya hau mahaifinsa da kanwarsa ‘yar shekara 7 da haihuwa da sara wanda hakan yayi sanadin ajalinsu. Shi ma daga bisani ya hallaka kanksa" Kakakin ta shaida.
Ta kara da cewa ya zuwa yanzu hukumar tana cigaba da bincike sai dai har yanzu bata san adadin mutanen da suka ji rauni ba.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng