Sauya sheka daga APC bai damuna ko kadan - Buhari

Sauya sheka daga APC bai damuna ko kadan - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yawan sauya sheka da jam’iyyar APC mai mulki ta fuskanta kwanan nan baya damun shi ko kadan.

A cewar wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya saki a ranar Litinin, shugaban kasar yayi Magana a daren ranar Lahadi da yake amsa wata tambaya a lokacin hira da mutanen Najeriya a Togo a ofishin jakadancin Najeriya, Lome.

An tattaro inda Buhari ke cewa shi bai damu da yawan sauya sheka ba saboda yawancin yan Najeriya sun gamsu da kokarin gwamnatinsa.

Sauya sheka daga APC bai damuna ko kadan - Buhari

Sauya sheka daga APC bai damuna ko kadan - Buhari

“Ban damu da yawan sauya sheka ba. Talakawan Najeriya sun yi na’am da mu sannan suna kare mu. Ina baku tabbaci, maiyawan yan Najeriya a gida sun gamsu da kokarinmu,” cewar shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Abun dariya ne APC bata so Dogara ya bar jam’iyyar – Yan majalisar wakilai

Da yake nuna jin dadi wajen ganin yan Najeriya da suka yi tafiya daga yankuna biyar na Togo domin yi masa maraba a Lome, Buhari yace ya yi farin ciki da jin suna yabama kokarin gwamnatinsa.

Ya basu tabbacin cewa gwamnatinsa na cigaba da jajircewa wajen gudanar da alkawaran zabe uku da ta dauna na samar da tsaro, inganta tattalin arziki da kuma yakar cin hanci da rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel