Ba don ni ba, da Buhari bai yi aiki da Tinubu ba Inji Buba Galadima
- Na kusa Buhari a da ya fasa kwan yadda Buhari ya hada-kai da Tinubu
- Buba Galadima yace su ne su ka shawo kan Buhari har aka kafa APC
Mun samu labari cewa Buba Galadima ya bayyana mafarar alakar Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Tsohon Sakatare na CPC ne yayi fashin bakin yadda aka yi kafin zaben 2015 a kasar.
Injiniya Buba Galadima a wata doguwar hira da yayi da Mujallar TELL ya bayyana cewa da farko Buhari bai da niyyar aiki da Bola Tinubu a lokacin yana ACN, sa’ilin kuma Shugaba Muhammadu Buhari su na Jam’iyyar CPC.
Buba Galadima ya bayyana cewa shi ne kashin bayan hada kan da Jam’iyyun adawar kasar su kayi. Galadima yace ba zai fadawa Duniya asalin abin da ya wakana ba amma Buhari bai so yayi aiki da Tinubu ba da farko.
KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya ci wasu kudi garabasa daga Turai
Tsohon Magoyin bayan Shugaba Buhari ya kalubalanci Shugaban kasar ya musanya wannan magana. Galadima yace shi yayi ruwa yayi tsaki har aka tsaidaFarfesa Yemi Osinbajo a matsayin Mataimakin Shugaba Buhari a 2014.
Galadima ya nuna cewa Shugaba Buhari ya kusa kai ga zaben wani dabam a matsayin Mataimakin sa inda ya kara da cewa Buhari ba zai yi nasara a 2019 ba. Galadima yace dole ya soki Buhari don kuwa akwai gyara a mulkin sa.
Dazu kun ji cewa Sanata Kwankwaso yayi magana game da sha’anin tsaro yace abin ya isa haka ya nemi Gwamnatin Buhari ta shawo kan kashe-kashen. Wasu manyan Sanatocin Arewa irin su Shehu Sani sun koka game da rikicin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng