Aikin Hajji: Saudiyya zata rage gurbin mahajjatan Najeriya a shekara mai zuwa saboda dalili 1 tak

Aikin Hajji: Saudiyya zata rage gurbin mahajjatan Najeriya a shekara mai zuwa saboda dalili 1 tak

- Saboda karancin mahajjata masu sauke farali a bana, Najeriya na shirin fuskantar barazana

- Matukar dai ba'a samu kari a masu niyyar zawa kasa mai tsarki to tabbas za'a rage gurbin Najeriya domin bawa wasu kasashen

Najeriya na iya fuskantar kalubale a shekara mai zuwa game da aikin Hajji sakamakon gaza samun adadin mahajjatan da zasu ziyarci kasa mai tsarki da ake bukata a bana.

Aikin Hajji: Saudiyya zata iya rage gurbin mahajjatan Najeriya a shekara mai zuwa saboda dalili 1 tak
Aikin Hajji: Saudiyya zata iya rage gurbin mahajjatan Najeriya a shekara mai zuwa saboda dalili 1 tak

A bana dai Najeriya ta samu gurbin mutane dubu 100 amma har ya zuwa yanzu mutane dubu 32 ne kacal suka samu damar kamalla komai domin zuwa sauke faralin, wanda hakan koma baya ne matuka ga wannan kasa.

Bayanin hakan yana fitowa ne daga bakin Ambasada Usman mataimakin shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar Kano kuma shugaban kamfanin shirya zirga zirga na Darma, a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa.

Jakadan ya ce ya zuwa yanzu hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON tana da bayanan mahajjata dubu 32 ne kacal, sai kuma ‘yan jirgin yawo su dubu 16 amma ba a sani ba ko ‘yan jirgin yawon zasu karu nan gaba tunda har yanzu ba a rufe sayar da kujerar zuwa aikin hajjin ba.

Hukumar Saudiyya zata iya rage gurbin da take bawa Najeriya domin karawa wasu kasashe wanda nasu gurbin ya musu kadan, amma Ambasadan ya ce a nasa tunanin wannan koma bayan baya rasa nasaba da karin kudin zuwa aikin hajjin.

KU KARANTA: Burin Dangote daya da ya rage a duniya na sayen Arsenal ya kusa cika

Idan aka yi duba da shekarun da suka gabata Najeriya na samun adadin mahajjata kimanin dubu 80 zuwa 90 wanda zasu je aikin hajji amma abin mamaki a wannan karon bai kai ko kashi uku cikin goma bane zasu hallarci kasa mai tsarkindon sauke farali.

Jakadan Najeriyar Usman yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa na mai adalci, don ganin yayi wani abu wajen don a rage kudin kujerar aikin hajjin saboda mutane da dama su samu zarafin zuwa sauke faralin.

A wani cigaban kuma, hukumar aikin Hajji ta kasa ta gargadi maniyyata da kada su wuce tsawon kwanaki takwas a garin Madina.

Wannan gargadi ya biyo bayan sanawar da hukukomin Saudiyya ta fitar game da kwanakin da za’a yi a lokacin aikin hajjin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa ana sa ran mahajjatan zasu baro garin na Madina zuwa Makkah bayan shafe kwanaki takwas.

Ya zuwa yanzu akwai mahajjata kimanin dubu 1,946 a garin Madina wanda yan asalin jihar Kogi, Nasarawa, Kaduna da Kwara ne.

Rahotan da NAN din ta rawaito ya bayyana cewa Alhazai 556 ne daga jihar Kaduna suka sauka a Madina, sai kuma 552 da suka fito daga jihar Kwara da suma suka sauka a kasar mai tsarki tun a ranar Juma'ar data gabata.

Kafin tafiyar tasu akwai mahajjata 446 daga Jihar Kogi, da 382 daga Jihar Nassarawa wanda tuni suka isa.

Hukumar ta ce dalilin da yasa za a kai maniyyatan Madina ba komai bane face domin ganin wuraren tarihi ne tare da yin ibada a Masallacin Manzon Allah SAW.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng