Za’a koma gidan jiya: Wahalar mai zata dawo

Za’a koma gidan jiya: Wahalar mai zata dawo

- Matsananciyar wahalar man Fetir din da aka sha a baya ta wat da watanni na shirin dawo

- Yanzu haka ma har wasu 'yan kasuwa sun karawa man farashi

Kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas ta kasa NUPENG reshen jihar Akwa Ibom, ta shiga yajin-aikin sai baba ta gani a ranar asabar, wanda hakan ka iya jawo karancin man fetur a jihar.

Za’a koma gidan jiya: Wahalar mai zata dawo
Za’a koma gidan jiya: Wahalar mai zata dawo

NUPENG dai ta yi hakan ne domin marawa 'yan'yan kungiyarta baya dake aiki da wani kamfanin mai mai zaman kansa na Universal Energy Resources Ltd.

Kungiyar ta datse jigilar mai jihar tun daga ranar 23 ga watan Yulin da muke ciki, wanda hakan ya sanya farashin man fetur tashin gwauron zabi, inda ake siyar da lita guda kan Naira 160 zuwa 180.

KU KARANTA: An kone daya daga cikin 'yan fashin da suka kashe wata kyakykyawar budurwa, duba hoto

Amma sai dai a nata bangaren gwamnatin jihar tayi kira ga jama'ar jihar da su kwantar da hankulansu game da yajin-aikin saboda akwai isasshen man da zai kai tsawon sati daya ana amfani da shi kafin a samo bakin zaren warware yajin-aikin.

Hakan na kunshe ne cikin wani jawabi da mai baiwa gwamnan jihar shawara game da harkokin da suka shafi man Fetur da iskar gas Obong Essien Esema ya yayi, inda ya gargadi yan kasuwa wajen ganin basu yi amfani da wannan damar ba wajen cusgunawa al'umma ta hanyar kara farashin man fetur din wanda ka iya jefa mutane cikin wani hali.

Za’a koma gidan jiya: Wahalar mai zata dawo
Za’a koma gidan jiya: Wahalar mai zata dawo

Ya ce "Bai kamata wasu suyi amfani da wannan damar don cimma bukatarsu ba, domin hakan ba yana nufin gazawar gwamnati bane ko kuma wata hukuma a karkashin gwamnatin ba", cewar mai bawa gwamnan shawara.

"Mun samu bayanai cewar yan kasuwa suna karawa kowace litar mai farashi, ko kuma su boye man baki daya domin samun riba mai gwabi".

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel