Shugaba Buhari zai ziyarci 'Kasar Togo tare da Ministar Kudi, Kemi Adeosun
Da sanadin shafin jaridar Daily Nigerian mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi zai yi sallama da Birnin Abuja tare da Ministar sa ta kudi, Mrs Kemi Adeosun, inda za su halarci wannan babban taro a birnin Lome na jamhuriyyar 'Kasar Togo.
Duk da takkadama ta zargin Ministar akan takardar ta bogi dake nuna shaidar yiwa kasa hidima, shugaba Buhari ya yi kunnen Uwar Shegu zai tasa keyar Ministar sa zuwa wasu muhimman taruka a birnin na Lome.
Tun makonni da shude na bujurowar wannan takaddama a kasar nan, ba bu wanda yace uffan tsakanin shugaban kasar da kuma Ministar da ake zargi duk da irin hura wuta da al'umma gami da kafofin watsa labarai ke yi a kasar nan dangane da wannan cin amana.
Legit.ng ta fahimci cewa, ana zargin Ministar ta kudi da fa'idantuwa da takardar bogi ta shaidar hukumar nan ta yiwa kasa hidima watau NYSC, sai dai hukumar kanta ta barranata da wannan takarda ta shaida da Ministar da gabatar.
Kamar yadda hadimi na musamman ga shugaban kasa akan hulda da manema labarai, Mallam Garba Shehu cikin wata sanarwa a ranar Asabar din da ta gabata ya bayyana cewa, shugaba Buhari zai gana da al'ummar Najeriya a ofishin jakadancin kasar a yayin isar sa kasar Togo.
A cewar sa, shugaban kasar a ranar Litinin zai kuma halarci taron kungiyar kasashen yankin Afirka ta Yamma domin tattaunawa kan al'amurran da suka shafi tsaro cikin kasashen dake cikin kugiyar watau ECOWAS (Economic Community of West African States).
KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta bayyana dalilin hana 'Yan takara gudanar da Yaƙin neman Zabe
Mallam Garba ya ke cewa, shugabannin zasu tattauna domin shinfida tsare-tsare da mataman magance annobar ta'addanci da kuma miyagun laifuka a gaba da iyakokin kasashen.
Idan mai karatu bai manta ba, a ranar 29 ga Yunin da ta gabata ne shugaba Buhari yayi na'am tare da amsa goron gayyatar wannan babban taro yayin da shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar na Togo, Faure Gnassingbe ya ziyarce sa a jihar Katsina.
Kazalika a can birnin na Lome, tawagar shugaba Buhari za ta halaci taron tattaunawa kan kudi na bai daya cikin kasashen na ECOWAS da ake sa ran kaddamarwa zuwa shekarar 2020.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng