Sanata Shehu Sani ya fadi dalilai 5 da suka sa zai fice daga jam'iyyar APC

Sanata Shehu Sani ya fadi dalilai 5 da suka sa zai fice daga jam'iyyar APC

Yayin da ake ta kara matsewa shekarar zabe a Najeriya ta 2019, siyasa a dukkan lungu da sako kuma a kowane mataki na ta kara zafafa musamman ma a tsakanin masu neman kujeru daban-daban.

Wannan ne ma ya sa kamar dai yadda masu fashin bakin siyasa ke bayyanawa ake samun yawan sauyin sheka a tsakanin jam'iyyun kasar.

Sanata Shehu Sani ya fadi dalilai 5 da suka sa zai fice daga jam'iyyar APC
Sanata Shehu Sani ya fadi dalilai 5 da suka sa zai fice daga jam'iyyar APC

KU KARANTA: EFCC ta biyo ta kan surukin Obasanjo

Legit.ng ta samu cewa sai dai kamar yadda ake samu a mafi yawancin lokutta, yan siyasar idan za su sauya sheka, sukan ayyana wani rashin adalci ko kuma rashin kyautawar da suke ganin anyi masu a matsayin dalilin su na yin hakan.

Duk da dai Sanata Shehu Sani dake zaman Sanatan dake wakiltar al'immar jihar Kaduna ta tsakiya bai canza sheka ba, amma dai ya bayyana wasu dalilai da yace sun kusa su sa ya fice ya bar jam'iyyar.

Ga dai dalilan nan kamar haka:

1. Yace Gwamnan jihar Nasiru El-rufai ya sanya an kore shi daga jam'iyyar ta APC bisa zalunci.

2. Yace 'yan bangar da yake tunanin an turo su ne sun kai hari ofishin sa har sau 5.

3. Yace Gwamnan jihar ya so ya laka masa laifin kisan kai.

4. A duk laifukan nan yace ba wanda yayi maga sai mataimakin jam'iyyar na kasa da shi kuma gwamnan ya sa aka rushewa gida.

5. Yace abokan siyasar sa da kuma al'ummar mazabar duk sun matsa masa lamba kan ya canza jam'iyya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng