2019: ‘Dan Majalisar APC ya nemi a biya sa kudi ya koma PDP

2019: ‘Dan Majalisar APC ya nemi a biya sa kudi ya koma PDP

Labari ya iso gare mu cewa wani fitaccen ‘Dan Majalisa daga Arewacin Najeriya ya bayyana sharadin sa na ficewa daga Jam’iyyar APC mai mulki ya dawo PDP. Sharadin da ‘Dan Majalisar ya bada ya ba sauran ‘Yan Majalisa mamaki.

2019: ‘Dan Majalisar APC ya nemi a biya sa kudi ya koma PDP
Wani 'Dan Majalisar Najeriya na neman Miliyoyin kafin ya koma PDP

Jaridar The Cable ta bayyana cewa wani Sanata daga Arewa maso Yammacin Kasar nan ya nemi a biya sa Naira Miliyan 100 idan har Jam’iyyar PDP na so ya sauya sheka. Jam’iyyar adawar dai tayi watsi da wannan roko na sa.

KU KARANTA: Wani Sanata ya tona asirin makircin da ake kullawa Buhari

A cikin kwanan nan Shugaban Majalisar Dattawa ya sanar da cewa wasu ‘Yan Majalisa sun sauya sheka zuwa Jam’iyyar adawa na PDP. Yanzu dai akwai wani Sanata da yake neman barin Jam’iyyar APC idan aka cika masa aljihun sa.

Wani Sanata daga Kudancin Kasar nan ya nuna cewa sun yi mamaki da su ka ji cewa Takwaran na su zai sauya-sheka idan har aka ba sa kudi. Jaridar The Cable din ba ta iya bayyana mana sunan wannan Sanata da ake magana ba.

Yanzu dai babu tabbacin cewa an biya ‘Yan Majalisar da su ka koma PDP wasu kudi na barin Jam’iyyar APC mai mulki. Shi dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wa masu sauya shekan addu’ar Allah ya bada sa’a a zaben 2019.

A Majalisar Wakilai ma akwai wadanda su ka fice daga Jam’iyyar APC. ‘Yan Majalisun sun hada da: Emmanuel Orker-Jev, Sani Rano Barry Mpigi, Ali Madaki, Hassan Saleh, Danburam Nuhu. Mark Gbilah, da Hon. Razak Atunwa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng