Wasu ‘Yan Majalisan APC ba su amsa goron gayyatan Shugaba Buhari ba
A shekaran jiya ne ‘Yan Majalisar da ke karkashin Jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Dattawa su ka gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin dare a fadar Shugaban kasa na Aso Villa.
Sai dai wasu manyan Sanatocin APC ba su samu zuwa wajen wannan taro ba wanda hakan ya jawo ‘yan ce-ce-ku-ce. Sanata Ahmed Lawan ne yayi magana a madadin Sanatocin Jam’iyyar a gaban Shugaban kasa Buhari.
Ga Sanatocin da ba su halarci wannan zama ba:
1. Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya zame a lokacin da aka yi wannan zama. Saraki da har yanzu yana Jam’iyyar APC ya dai tabbatar da cewa akwai yiwuwar ya tsere daga Jam’iyyar. Sauran Sanatocin Kwara dai tuni su ka sauya-sheka.
KU KARANTA: Shugaban APC ya gargadi wasu 'Yan cikin Jam'iyya
2. Ahmad Sani
Sanata Ahmad Sani Yariman-Bakura bai halarci wannan taro ba. An zauna ne da Shugaban Kasa da Sanatoci 42 da Shugaban Jam’iyya da Sakataren Gwamnati. Sanatan na Zamfara bai cikin wadanda aka yi wannan zama da su a makon nan.
3. Olusola Adeyeye
Sanata Olusola Adyeye wanda yana cikin manyan ‘Yan Majalisar bai samu halartar wannan zama ba. Sanatan na Osun dai bai ce ya bar Jam’iyyar ba amma an nemi sa sama da kasa an rasa a lokacin da Shugaba Buhari ya gana da Sanatocin APC.
Wadanda su ka halarci taron sun hada da irin su Sanata Aliyu Wamakko, Abdullahi Adamu, Bala Ibn Na’Allah, Kabiru Gaya, Adamu Aliero, Ibrahim Gobir, Andy Uba, Andrew Uchendu, da Aliyu Sabi Abdullahi da dai wasu Sanatocin da dama.
Har da irin su Sanata Shehu Sani na Kaduna aka gana da Shugaban Kasar. Shi ma Sanata Soji Akanbi da yace ya bar Jam’iyyar ya lashe aman sa sai ga shi a wajen taron inda yace ya dawo inda ya fi wayau tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng