Wata Mata ta jefa jikarta cikin rijiya saboda tsananin kishi da Uwarta

Wata Mata ta jefa jikarta cikin rijiya saboda tsananin kishi da Uwarta

Wata mata mai suna Aisha Ibrahim mai shekaru 55 ta shiga hannun jami’an Yansanda bayan ta halaka jikanta mai shekaru biyu a rayuwa ta hanyar jefa shi cikin rijiya a kauyen Karaya Fulani dake kamar hukumar Rafi na jihar Neja.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Aisha ta daure kafafuwar karamar yarinyar, sa’annan ta tsundumata cikin wani rijiya dake gidansu, duk dan ta kuntata ma mahaifiyar yaron, wanda take auren Danta Bello Ibrahim, ma’ana dai surukarta.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Legas za ta fara biyan Limamai da Malamai Albashi

Rahotanni sun bayyana wannan mummunan lamari ya faru ne a lokacin da Bello ya fita tare da matarsa zuwa wani kauye, inda suka bar diyar tasu a hannun kakarta, sai dai dama an dade ana takun saka tsakanin surukan biyu.

Wata Mata ta jefa jikarta cikin rijiya saboda tsananin kishi da Uwarta

Aisha

Aisha ta bayyana cewa tun bayan da Danta Bello ya yi aure matsaloli suka tasowa tsakaninta da Matarsa, kuma ta yi ta yi da shi akan ya saki Matar, amma yaki ji, matsalar har ta kai ga suna cacar baki da kuma zagin juna.

“Na fada ma mijina ya fada ma yaron nan ya saki Matarsa, amma yaki ji, matarsa tana yawan zagina, ni kuma naga babu hanyar da zan bi na rama abinda take min face na kashe yarta, don haka na daure kafafun yarinyar a jefata cikin rijiya, domin ta ji zafi kamar yadda nake ji.

“Muna zaman lafiya yaronnan ya auro matarnan, yayan 14, kuma gida daya muke zama dukanmu, don haka babu yadda za’ayi wata ta shigo gidanmu ta tayar mana da hankali, na dade ina wahala da iyalina, don haka zan yarda da wannan ba.” Inji Aisha.

Da aka tambayeta ko tana dana sanin kisan gillar da ta ma jikarta, sai Aisha yar asalin karamar hukumar Funtua tace: “Sharrin shaidan ne, ban san lokacin da na aikata hakan ba, fatana kawai shine Allah ya gafarta min.”

A nasa jawabin, Kaakakin rundunar Yansandan jihar Neka, Muhammadu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace wanda ake zargi ta amsa laifinta, kuma ta yi nadamar abinda ta aikata, amma yace zasu gurfanar da ita gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel