Yan Majalisar da suka koma PDP za su yiwa Buhari aiki ne — Fadar shugaban kasa

Yan Majalisar da suka koma PDP za su yiwa Buhari aiki ne — Fadar shugaban kasa

Mai ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin majalisa, Sanata Ita Enang ya bayyana cewa wasu daga cikin 'yan majalisar APC da suka koma PDP sun tabbatar da cewa za su taimakawa Shugaba Buhari wajen lashe zaben 2019.

Ya ce, 'yan majalisar ba su da wata rashin jituwa da Shugaba Buhari illa da shugabanni jihohinsu don haka sun nuna cewa a shirye suke su bayar da gudunmawarsu wajen tazarcen Buhari.

Yan Majalisar da suka koma PDP za su yiwa Buhari aiki ne — Fadar shugaban kasa
Yan Majalisar da suka koma PDP za su yiwa Buhari aiki ne — Fadar shugaban kasa

A wani lamari na daban, Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, babin jihar Anambra, Cif Damian Okeke ya gargadi majalisar dokokin kasar akan duk wani yunkuri na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Okeke yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Awka, ya ba da shawarar cewa hanyar mafi cancanta da ya kamata a bi wajen cire shugaban kasar, shine ta hanyar zabe.

KU KARANTA KUMA: Ina iya barin jam’iyyar APC – Gwamnan jihar Kwara

Ya ci gaba da cewa duk wani makirci don tsige Buhari zai iya haddasa rikicin siyasa a kasar wadda yana iya zuwa ga juyin mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng