An nada sabon jakadan Najeriya a birnin New York
- Ya maye gurbin tsohon jakadan ne wanda ya rasu ranar Lahadi.
- Yayi alkawarin kawo cigaba a bangaren jakadancin Nageriya.
Benaoyagha Okoyen ya karbi aiki a matsayin karamin jakadan Najeriya a birnin New York.
Okoyen dai ya maye gurbin tsohon jakada Mr Tanko Suleiman wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan kwanaki kadan bayan dawowar sa daga rangadi a birnin na New York, inda yayi ritaya a 27 ga watan Afrilun da ya gabata.
DUBA WANNAN: Wata duniya zata sakko kusa da tamu ranar 31 ga wannan watan - NASA
Sabon jakadan Najeriyan ya taba aiki da ofishin jakadanci na birnin New York a shekarar 2015.
Okoyen yayi alkawarin kawo cigaba a bangaren jakadancin ga 'yan Najeriya.
Ya tabbatar da kawo gagarumin cigaba akan yanda ake bida 'yan Najeriya a ofishin jakadancin.
Okoyen yana fatan cimma hakan ta hanyar zaunawa da kwararru a ofishin jakadancin dan kawowa Najeriya canji.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng