Rashin aikin yi, da tsadar rayuwa sune babbar matsalar Najeriya

Rashin aikin yi, da tsadar rayuwa sune babbar matsalar Najeriya

Babbar matsalar Najeriya a yanzu sune, rashin aikin yi da kuma matsalar tsadar rayuwa, a sanarwar da National Bureau of Statistics ta fitar

Rashin aikin yi, da tsadar rayuwa sune babbar matsalar Najeriya

Rashin aikin yi, da tsadar rayuwa sune babbar matsalar Najeriya

Babbar matsalar Najeriya a yanzu sune, rashin aikin yi da kuma matsalar tsadar rayuwa, a sanarwar da National Bureau of Statistics ta fitar.

A cewar hukumar, mafi yawancin 'yan Najeriya sun yarda cewar inda ace gwamnati zata kawo karshen rashin aikin yi a kasar nan, da an samu rangwame sosai a sauran matsalolin dake addabar kasar.

DUBA WANNAN: Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau

A wani taro da hukumar ta gabatar a ranar Larabar nan da ta gabata, wanda ta gayyato wasu manyan hukumomi na kasar, Daraktan hukumar na kasa Isiaka Olanrewaju, ya ce, a yanzu haka cin hanci da rashawa ba shine matsalar Najeriya ba.

Ya ce bayan hukumar su ta gabatar da bincike akan yawan 'yan Najeriya, sun gano cewar babbar matsalar Najeriya a yanzu ita ce matsalar rashin aikin yi.

Olanrewaju ya ce, "Bayan matsalar cin hanci da rashawa dake addabar kasar nan, mun saurari ta bakin jama'a akan matsalar dake addabar kasar nan, mun samu cewar matsalar rashin aikin yi ita ce ta farko a kasar nan, daga nan sai matsalar tsadar rayuwa, inda matsalar cin hanci da rashawa ta zo a matsayin ta uku.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel