Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau

Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau

- An haifi Sarauniya Amina a shekarar 1533, a garin Zazzau, wanda a yanzu haka babban gari ne a Najeriya

- Mahaifanta masu arziki ne sosai, wadanda suke kasuwancin sayar da dawakai, karafa, tufafi, goro, da kuma gishiri

Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau
Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau

An haifi Sarauniya Amina a shekarar 1533, a garin Zazzau, wanda a yanzu haka babban gari ne a Najeriya.

Mahaifanta masu arziki ne sosai, wadanda suke kasuwancin sayar da dawakai, karafa, tufafi, goro, da kuma gishiri.

Bayan da mahaifinsu ya rasu, sai ya yayanta ya haye kan karagar mulkin garin, inda ya gaji sarautar mahaifin nasu.

Sai dai kuma wani abin mamaki shine, ganin yanda Amina ta zabi wata hanya daban, ba irin ta ‘ya’yan Sarauta ba. Amina ta zabi ta dinga daukar horon yaki domin ta zama jaruma, dalilin da ya saka manyan dakarun yakin garin Zazzau suke girmamata.

Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau
Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau

Bayan yayanta ya rasu, Amina ce ta dare kan karagar mulkin garin, inda ta zamo Sarauniyar farko ga al’ummar garin.

Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau
Takaitaccen tarihin Sarauniya Amina ta Zazzau

Amina ta jagoranci yakinta na farko bayan watanni kadan da hawan ta karagar mulki. Ta rinka samun nasarori akai-akai tare da wasu dakarun sojojinta su dubu 20 da suke karkashin ikonta.

DUBA WANNAN: An tasa keyar Dino Melaye kotu, saboda yayi kokarin hallaka kansa

An ce a duk karshen yaki ta kan zabi namiji a garin, bayan ta kwanta dashi na kwana daya sai ta bada umarnin a kashe shi washe gari.

Yanzu haka a Najeriya an fi saninta da mace mai kamar maza, kuma ta nuna wa mata yanda suke da karfi da kwazo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel