Karshen alewa kasa: Dubun wani attajirin Kano dake luwadi da kananan Yara ta cika

Karshen alewa kasa: Dubun wani attajirin Kano dake luwadi da kananan Yara ta cika

Dama bahaushe na cewa rana dubu na barawo, rana daya kuwa na mai kaya, anan ma Allah madaukakin sarki ne ya tona asirin wani hamshakin dan kasuwan jihar Kano da ya shahara wajen aikata luwadi da kananan Yara, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba 25 ga watan Yuli ne wata Kotun majistri dake jihar Kano ta aika da wannan attajiri, Balarabe Habibu zuwa gidan Yari sakamakon zarginsa da ake yi da yin luwadi da wani yaro mai shekara Tara.

KU KARANTA: Karyar banza: Amurka ta soki kasashen Musulmai kan rashin tallafa ma Falasdinu

Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Pogu Lale ya shaida ma Kotun cewa Habibu mai shekaru 41 mazauni a unguwar Dullurawa ya aikata luwadi, wanda hakan ya saba ma sashi na 284 na kundin hukunta manyan laifuka.

Dansandan yace mahaifin wannan yaro mai suna Muratala Sa’idu tare da mahaifiyarsa Aisha Khalid ne suka kai karar wannan mutumi zuwa ofishin Yansanda dake Jakara a ranar 6 ga watan Yuli.

“A wannan rana ne suka lura yaron nasu da kyar yake tafiya, amma da suka tambayeshi sai ya bayyana musu gaskiya, cewa Habibu ne yake kais hi wurare da dama kuma yake luwadi da shi a wadannan wurare.” Inji Pogu.

Sai dai abinka da wanda ake tuhuma, nan take a gaban Kotu ya musanta wannan zargi, jin hakan ya sanya Alkalin Kotun, Muhammad Jibril ya bada umarnin a garkame masa shi har sai ranar da za’a cigaba da shari’a.

Daga karshe Alkali Jibril ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 20 ga watan Satumba, domin samun shawara daga ofishin babban jami’i mai shigar da kara na jihar ma’aikatar shari’ar jihar Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel