NYCN: An zabi Bello Shagari a matsayin Shugaban Matasan kasar nan

NYCN: An zabi Bello Shagari a matsayin Shugaban Matasan kasar nan

- Bello Shagari ya zama sabon Shugaban Majalisar Matasa na Najerya

- Shagari Mai shekara 30 a Duniya jikan tsohon Shugaban kasar nan ne

Mun samu labari cewa kwanan nan ne Bello Shagari ya zama Shugaban Kungiyar NYCN ta Matasan kasar nan. Bello Shagari ne yayi nasara a zaben da aka yi inda doke wani Mustafa Abullahi da kasa.

NYCN: An zabi Bello Shagari a matsayin Shugaban Matasan kasar nan
Bello Shagari daga Sokoto ya zama Shugaban Matasa

Majalisar NYCN ta Matasan da ke Najeriya ta zabi Bello Shagari wanda Jika yake wurin tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari. Shagari ya lashe zaben ne da kuri’a 8 rak kamar yadda Jaridar Kasar nan NewsDigest ta rahoto.

KU KARANTA: Shugaba Buhari bashi da ikon dakatar da binciken da ke kan Saraki

Matashin mai shekaru 30 a Duniya ya doke wasu ‘Yan takarar inda ya zama sabon Shugaban NYCN wanda ita ce lemar da ta ke rike da Matasa a Najeriya. Malam Bello Shagari ya samu kuri’u 249 ne a zaben da aka yi kwanan nan.

Shi kuma Mustafa Abdullahi Asuku wanda ya zo na biyu a zaben ya samu kuri’u 241 ne. Asuku ya sha kasa ne da kuri’un da ba su kai 10 ba cikin mutane 500 da su kayi zaben. ‘Yan Arewa masi Yammacin Kasar ne su kayi takarara.

Sakamakon zaben ya nuna cewa an samu kuri’u har 15 da ba a dangwala su daidai ba. Wannan matashi Shagari dai shi ne Matashin farko da Arewa maso yammacin kasar da ya fara hawa wanann kujera ta Shugaban Matasa na Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng