APC ta rasa wasu bara-gurbi – Lauretta Onochie
Misis Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa Muhammaddu Buhari ta bayyana cewa jam’iyyar All Progressive Congress ta rasa wasu bara-gurbi.
Onochie da take maida martani akan sauya shekar yan majalisun dokokin Najeriya da yawa a jiya ta bayyana cewa "kamar yadda yake ga mutun mai tarin kiba dake kokarin ganin ya rage lamarin a tsawon rayuwarsa, APC ta rasa wasu bara gurbi.
"A yanzu APC ta kara lafiya sannan kuma hakan ya fiyema jam’iyyar APC, da ma kasar. Tsoron Adams Oshiomhole, shine farin nasara."
Sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) goma sha biyar ne suka sauya sheka a jiya Talata, 24 ga watan Yuli.
KU KARANTA KUMA: Oshiomhole zai tabbatar da nasarar Buhari a 2019: Fayemi
Sanatocin sune Rabui Musa Kwankwaso, Barnabas Gemade, Dino Melaye, Isa Hamman Misau, Lanre Tajouso, Shaaba Lafiagi, Mohammed Shittu da Ubali Shittu, Rafui Ibrahim, Suleiman Hunkuyi, Monsurat Sunmonu, Ibrahim Danbaba, Usman Nafada and Suleiman Nazif.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng