Karyar banza: Amurka ta soki kasashen Musulmai kan rashin tallafa ma Falasdinu

Karyar banza: Amurka ta soki kasashen Musulmai kan rashin tallafa ma Falasdinu

Tir, Allah wadaran naka ya lalace, kamar yadda jakin dawa ya fada da yaga jakin gida, Jakadiyar kasar Amurka a majalisar dinkin Duniya, UN, Nikki Haley ta soki kasashen Larabawa da sauran kasashen Musulmai akan cewa basu taimaka ma Falasdina, inji rahoton VOA.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Haley ya bayyana Musulman Duniya a matsayin masu kumfar baki ne, ma’ana a baki ne kadai suke tare da Falasdinawa amma ba a aikace ba, inda tace Falasadinawa na cikin mawuyacin hali, amma Musulmai sun zura musu ido.

KU KARANTA: Ana zaton wuta a mekera sai ga ta a masaka: Yansanda sun kama Sojoji da laifin satar Turansufoma

Karyar banza: Amurka ta soki kasashen Musulmai kan rashin tallafa ma Falasdinu
Nikky Haley

Haley ta yi wannan batu ne a gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin Duniya, inda tace hatta kasashen Turkiyya, Hadaddiyar daular larabawa da Kuwait sun kasa bada kudi ga hukumar da majalisar dinkin Duniya ta kafa don tallafa ma Falasdin.

Cikin bacin rai, Haley tace: “Iran, Algeria da Tunisia basu baiwa hukumar ko sisi ba a shekarar data gabata, Kasar Masar da Pakistan sun baiwa hukumar dala dubu ashirin ashirin, yayin da kasar Oman ta bada dala dubu dari shidda da sittin da takwas.

“Kasar China ta bada dala dubu dari uku da hamsin don tallafa ma Falasdinawa, sai kuma Rasha, wanda ta bada dala miliyan biyu, Turkiyya ta bada dala miliyan shidda da dubu dari bakwai, sai Amurka wanda ta bada dala miliyan dari uku da sittin hudu ga hukumar tallafa ma kasar Falasdin.” Inji ta.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, Haley ta bada tabbcin kasar Amurka ta zaftare tallafin da take baiwa Falasdinawa da dala miliyan dari uku, wanda a sanadiyyar wannan zaftara, Falasdinawa sun kara tsunduma cikin halin ni’yasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: