Rabe-raben mutane 5 da ba su kaunar Shugaba Buhari - Inji fadar Shugaban kasa
Yayin da farfajiyar siyasar Najeriya ke cigaba da zafafa musamman ganin yadda zabukan shekarar 2019 ke kara matsowa, ra'ayoyi mabambanta na ta kara fitowa a bainar jama'a na al'ummomi daban daban.
Wasu 'yan siyasar da ma 'yan kasar daga cikin talakawa dai na ganin babu wanda ke iya cetar kasar daga halin da ta shiga ciki sai shugaba Muhammadu Buhari yayin da wasu kuma ke ganin akasin hakan.
KU KARANTA: Wani dan kudu ya ba Buhari motocin kamfe din tazarcen sa har 31
Legit.ng ta samu daga daya daga cikin hadiman shugaban kasar ta fannin sadarwa, Bashir Ahmad ya zayyana rabe-raben mutane kala 5 da yace sune kawai ba su son shugaban kasar:
1. Masu tsoro ko kuma kaucewa biyan haraji
2. Wadanda gwamnatin ta kwacewa kadarori saboda tarin bashi
3. Jami'an gwamnatin da suka wawure dukiyar al'umma kuma yanzu haka suke fuskantar shari'a
4. 'Yan Najeriya da suke cima zaune da basu tabukawa kansu komai sai abunda 'yan siyasa suka basu.
5. 'Yan siyasar da suka san cewa tabbas ba za su samu tikitin takara a jam'iyyar ba zabe mai zuwa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng