‘Yan sanda sun yi nasarar kama wani kasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara

‘Yan sanda sun yi nasarar kama wani kasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara

Rundunar ‘yan sanda, reshen jihar Zamfara, sun dakile wani hari da ‘yan bindiga a kauyukan Chali da Gobirawa dake karamar hukumar Maru.

Kazalika jami’an ‘yan sandan sun yi nasarar kama kasurgumin dan ta’adda kuma shugaban ‘yan bindigar, wanda ya kasance da ne ga mashahurin dan ta’adda, Buharin Daji, da aka kashe a watannin baya.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Zamfara, Mista Kenneth Embrimson, ya sanar da hakan ga manema labarai yayinda yake bajakolin masu laifin.

‘Yan sanda sun yi nasarar kama wani kasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara; Abdulaziz Yari

Embrimson ya bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun yi kokarin kai hari wasu kauyuka biyu a ranar 23 ga watan Yuli, amma jami’an ‘yan sanda sun dakile yunkurin maharani.

Cikin gaggawa jami’anmu suka tafi kauyukan bayan samun rahoton abinda ke faruwa. Sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar kafin daga bisani su samu nasarar raunata tare da kama daya daga cikinsu yayin da ragowar suka tsere.

DUBA WANNAN: Batanci: Jami'an tsaro sun mamaye makarantar da dalibi ya zagi annabi

Daga bisani ne muka gano cewar dan ta’addar da muka kama, Zakoa Buhari, da ne ga kasurgimin dan ta’adda, marigayi Buharin Daji da aka kasha,” a cewar Embrimson.

An kama bindiga daya da alburusai a tare da Zakoa, kuma yanzu haka yana hannun hukumar ‘yan sanda inda yake bayar da muhimman bayanai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel