Wani Sanata daga cikin Sanatoci 15 da suka fice daga APC ya karyata ficewarsa

Wani Sanata daga cikin Sanatoci 15 da suka fice daga APC ya karyata ficewarsa

Awanni kadan bayan Sanatoci guda goma sha biyar na jam’iyyar APC sun sanar da ficewarsu zuwa jam’iyyar PDP, an samu wani daga cikinsu daya barranta da sauran Sanatocin tun ba je ko ina ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatan mai suna Rilwan Adesoji Akanbi ya bayyana haka ne a ranar Talata, 24 ga watan Yuli, inda ya karyata batun komawarsa PDP daga APC, kuma ya jaddada biyayyarsa ga APC, tare burin cigaba da zama a cikinta.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Buhari ya yi ma babban Sufetan Yansanda gayyatar gaggawa

Wani Sanata daga cikin Sanatoci 15 da suka fice daga APC ya karyata ficewarsa
Rilwan

Sanatan Rilwan ya bayyana bacin ransa tare da kaduwarsa da yadda ya ji shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya ambaci sunansa a cikin Sanatocin da suka yi odabo da jam’iyyar APC ta baba Buhari.

“Babu yadda za’ayi na rusa gidan da na taimaka wajen gina shi, ni dan Buhari ne dari bisa dari, kuma Tinubu ne Maigidana, haka zalika gwamnan jihar Oyo Ajimobi gwamnanane, kuma Yayana, duk masu yunkurin bata min suna sun ji kunya.” Inji shi.

Daga karshe Sanata ya bada tabbacin cewa zai kira taron manema labaru da nay an jaridu don bayyana ma Duniya kin amincewarsa da fita daga jam’iyyar APC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng