Duk mutum mai kima ba zai taba komawa jam'iyyar PDP ba - Kwamared Oshiomhole
Shugaban jam'iyya mai mulki ta APC a Najeriya Kwamared Adams Oshiomhole a ranar Litinin din da ta gabata a ce dukkan wanda ya san kima da mutuncin kansa to kau ba zai koma jam'iyyar adawa ta PDP ba.
Oshiomhole ya kara da cewa shi har yanzu baccin sa kawai yake da salaba domin barazanar da 'yan aware na tsagin jam'iyyar R-APC ko kadan bai kai na ya tada masa hankali ba.
KU KARANTA: "Buhari ya kwana da shirin barin Villa"
Legit.ng ta samu cewa Adams yayi wadannan kalaman ne jim kadan bayan kammala ganawa da shugaban kasa a fadar sa.
A wani labarin kuma, Shugaban hukumar dan dake kula da teku da hanyoyin ruwa a cikin Najeriya watau National Inland Waterways Authority a turance mai rikon kwarya mai suna Danladi Ibrahim ya bayyana cewa gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari za ta soma aikin yashe tekun Benue.
Danladi Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Legas inda kuma ya bayyana cewa hakan ya zama dole ne domin kara habaka ayyukan hada-hadar kasuwanci a kogin Baro.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng