Kifa daya kwala: Wani matashi ya yi ma abokinsa duka daya har lahira akan N100
Wani matashi mai suna Haruna ya halaka abokinsa Gaddafi ta hanyar yi masa kwakkwaran naushi guda daya bayan rikici daya kaure a tsakaninsu akan kudi naira dari, inda nan take ya fadi matacce a garin Abaji na babban birnin tarayya Abuja.
Wani shaidan gani da ido Ismaila Bala yace wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis din data gabata, a kasuwar dabbobin garin, inda yace abokan biyu sun taimaka wajen kamo wata Saniya da ta tsere yayin da ake tsaka da cinikinta.
KU KARANTA: Wani matashi ya zartar da hukuncin Zina akan wasu abokansa guda 2
Bayan an kamo dabbar, sai mai ita ya ciri naira 100a ya baiwa wanda ya kamota, anan ne fa cacar baki ya kaure a tsakaninsu akan wanene ya kamo dabbar, inda kowannensu ke ikirarin shi ya kamota, ana cikin haka sai guda ya kai ma dayan naushi a wuya, nan take ya tashi ya fadi matacce.
Ba tare da wata wata ba jama’an dake wajen suka diran ma Haruna, suna ta dukansa, har ma wasu suka caka masa wuka, da kyar Yansanda suka kwace shi, sa’annan suka umarceshi ya garzaya da Gaddafi zuwa Asibiti, a can ne likitoci suka tabbatar da ya mutu.
DPO na Yansandan Abaji, Tersoo Tile ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni suka mika gawar mamacin ga iyalansa domin su yi masa jana’iza, yayin da shi ma wanda yayi kisan yake kwance cikin mawuyacin hali a Asibitin koyarwa na jam’iar Abuja.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng