Ambaliyar ruwa tayi sanadin mutuwar mutune 13, muhalli 17,000 sun salwanta a Nijar

Ambaliyar ruwa tayi sanadin mutuwar mutune 13, muhalli 17,000 sun salwanta a Nijar

- Rayuka da dukiyoyi sun salwanta a bayan wata ambaliyar ruwa

- Dama dai majalisar dinkin Duniya tayi hasashen yiwuwar samun ambaliyar ruwan a kasar ta Nijar

Hukumar agajin gaggawa ta Majalisar dinkin Duniya OCHA ta sanar da cewa mutanen da yawansu ya kai 17,000 sun rasa muhallansu.

Ambaliya tayisanadin mutuwar mutune 13 muhalli 17,000 sun salwanta a Nijar

Ambaliya tayisanadin mutuwar mutune 13 muhalli 17,000 sun salwanta a Nijar

Sanarwar ta ce a ranar 18 ga watan na Yulin da muke ciki ne ruwan saman da aka sharara kamar da bakin kwatrya ya hadassa asarar rayuka da ta dukiyoyi a wasu yankunan kasar.

An kiyasta cewa fadin kasar noma kimanin 400 ta lalace sannan dabbobi 24,000 ne suka mutu a sakamakon ambaliyar.

BBC ta rawaito cewa, a tsakiyar watan da ya gabata ne majalisar dinkin Duniya ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar kasar Jamhuriyar Nijar zata fuskanci ambaliyar ruwan da ka iya shafar a kalla mutum 170,000 a jihohin Dosso da Niamey, inda kogin Nijar ya ratsa.

KU KARANTA: Barazanar yaki: Donald Trump ya mayarwa Hassan Rouhani martini mai zafi

Duk da cewa tsayin damina wata uku ne kadai kuma ba’a samun ruwa mai yawa, amma duk da haka kasar Nijar din na fuskantar matsalar ambaliya ruwa a 'yan shekarun baya-bayan nan.

Ko a bara ma sama mutune 50 ne suka mutu a wata ambaliyar ruwa, yayin da wasu 206,000 suka rasa matsugunansu,sannan kuma eka 9800 ta kasar noma ta salwanta.

Gwamnatin Nijar ta ce ta saka makudan kudade na kusan CFA biliyan uku tare da taimakon Bankin Duniya don gina shingayen da za su hana kwararowar ruwan zuwa gidajen da ke bakin kogin Nijar a Yamai, a matsayin riga-kafi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel