Ana zaton wuta a makera: An kama jami’an SARS 4 da laifin fashi da makami

Ana zaton wuta a makera: An kama jami’an SARS 4 da laifin fashi da makami

- Masu tsaron mutane sun buge da damfara ta hanyar tursasawa da tsoratarwa

- Jami'an SARS dama dai ana zarginsu da yawan keta ka'idar aikinsu ta hanyar cin zali da cin zarafin wadanda basu ji ba basu gani ba

An kori jami'an rundunar ‘yan sanda na SARS guda 4 sakamakon garkuwa da wani mai suna Chukwudi Godwin Odionye mazaunin yankin Ajagbandi da ke Jihar Legas, wanda aka fi sani da Bishop, tare da kwace masa kudi kimanin Naira miliyan 7.

Ana zaton wuta a makera: An kama jami’an SARS 4 da laifin fashi da makami

Ana zaton wuta a makera: An kama jami’an SARS 4 da laifin fashi da makami

Tun da farko dai Bishop ya rubuta korafinsa ne zuwa ofishin mataimakin babban baturen ‘yan sanda na kasa wato AIG Adamu Ibrahim, tare da bayyana masa cewa a ranar 4 ga watan Yuni ne ‘yan sandan na SARS dake Ikeja suka mamaye masa gidansa bisa zarginsa akan karyar karama da ya ke yi.

Yace: "Sun kamani amma a maimakon su kai ni ofishinsu, sai suka kai ni wani hotel dake unguwar Agege tare da tsare ni bisa karkashin kulawar daya daga cikinsu, tare da yi min barazana matukar ban basu hadin kai ba, to babu shakka za su kashe ni"

KU KARANTA: An yi zazzafar musayar wuta tsakanin Boko Haram da Sojojin Najeriya, kowanne bari sunyi rashi

"Kwana daya da tsareni din ne sai suka sake daukata zuwa Banki, inda suka saka ni na tura musu kudi kimanin Naira miliyan 7 a asusun daya daga cikinsu."

Da yake bayyana matsayar rundunar yan sanda akan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan shiyyar jihar Legas CS Dolapo Badmus, ya ce rundunar ta gudanar da bincike akan yadda al'amarin ya faru, inda ta binciko yadda wadannan jami'an ‘yan sanda na SARS su ka tsallake ka'idojin aikin dan sanda.

Ya kara da cewa tabbas sun kama wadannan jami’an da suka kai wanda suka kamoni Otal maimakon su kai shi ofishinsu.

A karshe ya bayyana cewa kwamitin ladabtarwa ya gabatar da rahoton bincike, inda aka sallami jami'an ‘yan sandan daga bakin aiki. An bayyana sunayen ‘yan sandan da abin ya faru da su da suka hada da Sajan Adeoye Adekunle da Adeniran Adebowale da Agbi Lucky sai kuma Odighe Hehosa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel