Wani ‘Dalibi ya zagi Annabi Muhammad a makarantar koyon shari’a da ke Legas
- Hatsaniya na shirin kaurewa a makarantar koyon aiki shari’a da ke Legas
- Wani ‘Dalibin Makarantar ne yayi wasu munanan kalamai game da Annabi
Mun samu labari cewa rikici na nema ya barke a makarantar koyon shari’a da ke Legas bayan da wani ‘Dalibi mai suna Madu Vitrus yayi batanci ga Manzon Allah Annabi Muhammad SAW.
Labarin ya zo mana daga Jaridar DAILY NIGERIAN ne inda ta rahoto cewa wannan ‘Dalibi Madu Vitrus ya aika wani mummunan sako na batanci ne ga Annabin Musulunci Annabi Muhammad ta kafar sadarwar nan na zamani na Whatsapp kwanan nan.
Yanzu haka ana kishin-kishin din wasu Musulmai masu kaushin ra’yin addini sun shirya ganin bayan wannan ‘Dalibi idan har Hukuma ba ta dauki matakin da ya dace ba. Har yanzu dai Hukumar Makarantar ba ta fito tayi magana ba tukun.
KU KARANTA: ‘Dalibin ABU zai hadu da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar.
Wani ‘Dalibin Makarantar ya bayyanawa Jaridar cewa ba za su amince da irin wannan wulakanci da ake yi wa fiyayyen halitta a Musulunci ba. Wannna ‘Dalibi da ke karatu a Makarantar da ke Garin Legas din dai ya nemi a sakaya sunan sa.
Kungiyar ‘Dalibai Musulmai na Makarantar ta koyon aikin shari’a sun nemi Hukumar makarantar ta hukunta masu zagin Annabi Muhammad SAW. Wasu dai yanzu sun yi dako su na jiran su hallaka wannan ‘Dalibi da zarar sun yi ido-hudu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng