Kaico: Wani lebura ya kashe Uban-gidansa tare da binne gawar don ya sace kudinsa
- Duniya ina zaki da mu ne? Akan kudin da ba su kai dubu dari ba ya kashe mai gidansa
- Mai gidan dai ya samu kudin ne bayan ya sayar da abin hawansa, amma ashe yaron ya sanyawa kudin arwa
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Borno sun damke wani matashi mai suna Inusa Abubakar, mai kimanin shekaru 19 da haihuwa bisa zarginsa da ake kan kisan mai gidansa da aka bayyana sunansa da Ba'Ana Bukar.
Tun farko dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Borno Mista Damian Chukwu ya bayyana cewa, wanda ake zargin yana sana'ar gini ne tare da mai gidansa, sannan ana zarginsa da yin amfani da wuka wajen kashe mai gidan nasa a lokacin da su ke tsaka da aikin gini a unguwar Pompomari da ke cikin birnin Maiduguri.
KU KARANTA: Tsaleliyar budurwa ta bayyana yadda dan uwanta ya tsiyayar mata da ido daya
Kwamishinan ya kara da cewa “Bayan da ya kashe shi ta hanyar daba masa wukar, sai yayi amfani da daya daga cikin kayan da su ke gini da su, ya haka rami tare da binne shi, daga nan kuma ya garzaya gidan mamacin inda ya kwashe masa kudi kimanin Naira 62,000"
Daga karshe shugaban ‘yan sandan ya ce sun gano wukar da ya yi amfani da ita wajen kashen mamacin tare kuma da kudin da ya sace.
Ana dai zargin kudin na abin wani hawan da mamacin ya sayar ne, inda shi kuma ya kyallara ido kansu har ta kai ga ya yanke shawarar aikata danyan aikin don kwashe su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng