Jam’iyyar APC ta shiga cikin uwar-bari a Jihar Adamawa bayan zuwan Atiku

Jam’iyyar APC ta shiga cikin uwar-bari a Jihar Adamawa bayan zuwan Atiku

- APC ta rasa wasu Kwamishinoni a Jihar Adamawa bayan zuwa Atiku

- Wasu manyan ‘Yan siyasa a Adamawa sun koma Jam’iyyar PDP yanzu

Akalla ba a kasara ba, za a samu Kwamishinoni da wasu Yan Majalisu da kuma manyan Shugabannin Jam’iyyar APC a kananan Hukukomi da su ka tattara su ka koma Jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa.

Jam’iyyar APC ta shiga cikin uwar-bari a Jihar Adamawa bayan zuwan Atiku

Guguwar Atiku ta rusa Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa

Kwamishinoni 8 ne ake sa rai sun sauya sheka daga Jam’iyyar APC mau mulki zuwa Jam’iyyar adawa ta PDP. Hakan na zuwa ne bayan da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya shiga Jihar ya kaddamar da shirin takara.

KU KARANTA: Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya tara jama'a a Yola

Atiku Abubakar ya hada wani taro kwanan nan a Garin Yola inda ya shirya yakin neman zaben Shugaban kasa. A dalilin haka ne wasu manyan ‘Yan siyasan da ake ji da su a Adamawa su ka fice daga APC su ka bi Atiku zuwa Jam’iyyar PDP.

Shugaban Jam’iyyar PDP Prince Uche Secondus ya bayyana cewa daga cikin Kwamishinonin da su ka bar PDP akwai Alhaji Ibrahim Mijinyawa da Alhaji Umar Daware. Shugaban na PDP yace wasu ma su na nan za su tsere daga Jam’iyyar ta APC.

Kwanaki dai kun ji cewa Sanatan da ke wakiltar Adamawa ta tsakiya a Majalisar Dattawa watau Abdulaziz Nyako ya fice daga Jam’iyyar ta APC shi ma. Haka kuma wani ‘Dan Majalisa da ke wakiltar Gombi a Majalisar dokokin Jihar ya sauya sheka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel